Sabon kawancen siyasar Nijar yayi maci cikin Yamai

Malam Seini Omar
Image caption Daya daga cikin 'yan takara shidda da suka kulla kawancen

Sabon kawancen siyasar da wasu yan takarar shugaban kasa shidda suka kulla a Jamhuriyar Nijar yayi wani maci a birnin Niamey domin tallata wannan kawance ga mazauna birnin da ma sauran kasa baki daya.

Gangamin da wannan kawancen yayi, ya bayar da dama ga shugabannin da su cudanya da juna da kuma saurn jamaa gabanin zaben da zaa yi ranar litinin mai zuwa.

A karkashin kawancen, mai suna ARN, yan takarar sun amince su idan har an kai ga zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, su marawa daya daga cikinsu baya.

'Yan takarar da suka kulla wannan yarjjeniya sun hada da tsohon shugaban kasa Alhaji Mahamane Ousmane na Jam'iyyar CDS Rahama da tsohon prime Minista Hamma Amadou na Moden-Lumana da kuma Malam, Seini Oumarou na MNSD -Nasara.

A halin yanzu dai Hukumar zabe mai zaman kanta a Niger, watau CENI ta bayyana cewar ta dauki dukkan matakan da suka dace domin ganin komai ya tafi lafiya lau a zaben shugaban kasa da na yan majalissun dokokin da zaa yi ranar litinin mai zuwa.

Haka nan kuma hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya PNUD / UNDP da ke tallafawa da kudi ta ce za ta bayar da gudummuwarta a kan lokaci.

Ko a jiya ma dai sai da shugaban gwamnatin mulkin soji Janar Salou Djibo, yayi wani taro da wakilan gwamnati da hukumar zaben da kuma masu bayar da taimako na kasashen waje domin yin bitar inda aka kwana a shirye shiryen zaben.