PDP ta ce za ta sake zaben fidda gwani a wasu Jihohin

Image caption PDP

Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta ce babu gudu ba ja da baya a shirinta na gudanar da sabbin zabukan fidda gwani na mukaman gwamna da 'yan majalisar dattijai a wasu jihohin kasar.

Bayanai sun ce jam'iyyar a yanzu ta fasa sake gudanar da zaben fidda gwani na kujerar gwamna a jihar Kogi, amma za ta sake gudanar da zaben fidda gwani na kujerar gwamna a jihar Kano.

Jam'iyyar ta kuma ce baicin zaben da za ta sake gudanarwa na wasu kujerun 'yan majalisar dattijai a kasar, nan gaba kadan za ta sake fitar da wasu jerin sunayen na kujerun majalisun wakilai da ma na jihohi inda nan ma za a sake gudanar da zaben fidda gwanin.

Hakan na faruwa ne kuwa duk da sanarwar da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fitar cewa sake zabukan fidda gwanin da PDP ke shirin yi haramtacce ne.

Jam'iyyar PDP dai ta dage cewa dokar zabe ta bata hurumin sake gudanar da zabukan.