Amurka ta bukaci samar da sauye sauye a Masar

'Yan sandan kwantar da tarzoma a Alkahira, babban birnin kasar Masar sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a kan dubban mutane dake son yin zanga zangar nuna kyamar gwamnati.

Mutanen sun hallara ne duk kuwa da barazanar da aka yi ta hukunta su

Can ma a yankin Suez , inda aka kashe uku daga cikin masu zanga zangar a jiya, an yi fito-na-fito.

Ministan cikin gida ya ce an kama mutane dari biyar cikin kwanaki biyu da suka wuce.

Amurka ta ce tana sa ido sosai kan abubuwan dake faruwa.