Kamanta gaskiya da adalci ne kawai zai kawar da rigingimu a Afrika

Mahalarta wata laccar da jaridar Daily Trust ta shirya a Abuja na Nijeriya sun bayyana cewa zai yi wuya kasashen nahiyar Afirka da dama su kauce wa rigingimun siyasa a kasashensu.

Sun bayyana cewardole ne shugabanni su sauya salon jagoranci ta hanyar kamanta adalci da gaskiya idan suna son gujewa abubuwan da ke faruwa a wasu kasashe irin su Tunisia da Masar .i

Masanan dai sun ce wajibi ne shugabanni su kyale al'umomi su zaba wa kansu wadanda suke so su shugabance su, kafin a samu zaman lafiya.