An shiga yini na hudu a zanga-zangar Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters

Hukumomin Masar na shirin tunkarar yini na hudu na zanga-zangar adawa da gwamnati.

BBC ta samu labarin cewa jami'an tsaro sun shaidawa shugaba Mubarak za su iya shawo kan duk wani tashin hankali da zai iya biyo bayan sallar Juma'a a yau.

Babbar kungiyar adawa ta 'yan uwa Musulmi ta ce za ta goyi bayan zanga-zangar ta yau duk da dai ba ta umarci magoya bayanta su fito kan tituna ba.

A daren jiya dai wani lauyan kungiyar ya ce mahukunta sun kama jiga-jiganta gudu hudu tare da wasu mabiya.

Wasu rahotanni na cewa an yi ta samun matsalar amfani da yanar gizo da wayoyin tafi da gidanka.

Wasu mutanen dai sun bayyana cewa sam sun kasa shiga shafukan yanar gizo, yayin kuma da wasu ke bayyana wasu matsalolin na daban.

Yanar gizo wato internet dai ta taka mahimmiyar rawa wajen hado kan masu zanga zanga a duk kasashen larabawa ciki har da kasar Masar, lamarin da ya yi ta janyo zanga zanga ta kwana da kwanaki.

Matsalolin da aka samu na kasa shiga shafukan yanar gizon dai zai iya takaita wasu jerin zanga zangar da ake kokarin shiryawa nan gaba.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta bayyana cewa za ta dauki gagarumin mataki akan duk wani wanda ya tada zaune tsaye bayan an idar da Sallar Juma'a.