Ana cigaba da zanga-zanga a Masar

Masu zanga-zanga a Masar Hakkin mallakar hoto reu
Image caption Masu zanga-zanga a Masar

Jam'iyyar NDP da ke mulkin Masar, ta ce a shirye take ta tattauna da jama'a da jam'iyyun 'yan hamayya, a wuni na ukku da aka kashe ana zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Sakatare Janar na jam'iyyar ta NDP, Safwat Al Sherif ya ce lokaci ya yi na saurare, amma kuma dimokuradiya da tana ka'idojinta da tsarinta.

Ahalin da ake ciki kuma, Babban dan hamayya na kasar, Muhammad Al Barada'i, wanda ya koma kasar, ya ce, ya kuduri aniyar shiga cikin zanga-zangar da zaa yi gobe Jumma'a, don nuna goyon baya ga bukatun jama'a na kyautata rayuwarsu.