An fitar da rahoto kan rikicin jihar Pilato

Jana'izar wasu mamata a Jos Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jana'izar wasu mamata a Jos

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil'ada ta Human Rights Watch ta fitar a yau akan rikicin Plateau ya ce mutane dari biyu ne aka kashe a rikicin daga watan Disamban 2010 zuwa yau.

Kungiyar ta ce an kashe mutanen ne a yunkurin daukar fansa kuma cikin wadanda aka kashe din har da yara kanana.

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta yunkura wajen kare fararen hula , kuma ta bari mai baiwa sakatare janar na majalisar dinkin duniya shawara akan kisan kare dangi ,wato Francis Deng, ya ziyarci jihar ta Pilato.