An yi sabbin tashe tashen hankula a Jihar Filato

Rahotanni daga jihar Filato a Nijeriya, na cewa an sami tashe-tashen hankula a wasu kauyuka dake karamar hukumar Barikin Ladi.

Bayanai dai sun nuna cewar an sami hasarar rayuka a wadannan tashe tashen hankula wadanda kawo yanzu ba a tabbatar da wadanda suka haddasa su ba

Bayanan dai na cewa lamarin ya fi kamari ne a kauyen Dorawar Babuje, inda aka yi ta kone-kone da kuma kashe-kashe tare da jikkata wasu da dama.

Haka nan Kuma an sami wani tashin hankalin a garin Tafawa Balewa dake jihar Bauchi.