Shirin zabe a Jumhuriyar Nijar

Tutar Jumhuriyar Nijar
Image caption Tutar Jumhuriyar Nijar

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijer wato, CENI ta ce komai ya kammala,wajen hada dukkan kayayyakinda ake bukata domin gudanar da zaben.

Shugaban hukumar zaben mai shara'a Ghousmane Abdourhamane ne ya tabbatar wa shugaban mulkin sojan Nijer din janar Salou Djibo da haka a yau din nan, lokacin da shugaban kasar ya kai wata ziyara cibiyar hukumar zaben domin jin inda aka kwana game da shirye-shiryen da ake yi.

A zaben kananan hukumomin da aka gudanar a farkon wannan watan dai an fuskanci matsaloli da dama da suka hada da rashin kai kayan aiki rumfuna zabe kan lokaci.

Ranar Litinin mai zuwa ne dai zaa gudanar daugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin Nijar din a shirin da ake yi na mayar da kasar bisa tafarkin Demokradiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabrairun bara.