Dubun dubatar mutane sun yi zanga zanga a Yemen

Masu zanga zanga a Birnin Sannaa
Image caption Masu zanga zanga a Birnin Sannaa

Dubun-dubatar mutane suna zanga-znga a Sana'a babban birnink kasar Yemen, inda suke kira ga shugaban kasarsu, Ali Abdullah Saleh, wanda ya shekara talatin yana mulki, cewa ya yi murabus.

Cike dai zanga-zangar take da kade-kade da bushe-bushe:

Masu zanga-znagar sun taru a wurare daban-daban a birnin suna rera cewa, "lokacin sauyi ya zo", inda suke hannunka-mai-sanda da juyin da aka yi a Tunisia, inda aka hambarar da shugaba Zainul Abidin bin Ali, can baya a wannan watan.

An bada rahoton yin wata zanga-zangar goyon bayan gwamnati, wadda jam'iyyar shugaban kasar ta shirya.

Rahantanni sun ce an tsaurara matakan tsaro amma masu zanga zangar ba su yi taho mu gama da jamian yansanda ba..

Ana dai ganin barkewar tarzomar nada nasaba da abubuwan da suka janyo tashen tashen hankula a kasashen Tunisia da kuma Masar wato talauci da rashin aikin yi da rashawa da kuma fushi da masu mulki.