Mahammancin kasar Masar

Mahammancin kasar Masar Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wakilin BBC Assad Sawey wanda 'yan sandan Masar suka nadawa duka

A lokutan 1960, Masar na taka mahimmiyar rawa a cikin kasashen Larabawa, musamman a fagen diflomasiyya da kuma tsaro.

Amma a yau, bayan shekaru 50, masu taka rawa a yankin Gabas ta Tsakiya su ne kasashen da ba na Larabawa wato Isra'ila da Turkiyya da Iran.

Duk da haka Masar na da tasiri ba wai kawai saboda tarihi ba. Girmanta da kuma karfin sojinta ya sa tana da karfin fada aji a yankin.

Kuma a yanzu tana daya daga cikin kawayen Amurka na kud-da-kud, ita ke biye ma Isra'ila a wajen samun taimakon soji daga Amurka.

Sai dai tana fama da matsalolin da sauran kasashen yankin ke fama da ita: talauci; karuwar yawan matasa, rashin aikin yi da karancin tsarin dimokradiyya.

An kifar da gwamnati a Tunisia, kuma al'amura sun ci gaba a yankin. Idan aka kifar da gwamnatin Hosni Mubarak, to lamarin zai zama abin duba wa.

Image caption Shugaba Hosni Mubarak ya shafe shekaru 30 yana mulki a kasar

Abin da babu tabbas shi ne idan gwamnatin ta fadi, wanene zai dauki ragamar.

Idan har gwamnatin Masar ta fadi, tasirin hakan ka iya yin nisa har zuwa Washington.

Ko wannan zai zamo wata dama ga kungiyoyin Isalama masu adawa da gwamnati?

Ko za a samu tashin hankali ko sojoji za su shigo domin tabbatar da doka da oda? Har yanzu ba mu kai nan ba tukunnan.

Don haka zanga-zangar ta Masar ke jan hankalin ofisoshin kasashen waje da dama ba wai kawai a Gabas ta tsakiya ba.

Karin bayani