An kashe dan takarar gwamnan ANPP a Borno

Borno Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Akwai babban kalubale a gaban rundunar 'yan sandan jihar ta Borno

Wasu 'yan bindiga sun harbe dan takarar gwamnan jihar Borno na jam'iyyar ANPP Modu Fannami Gubio, tare da wasu mutane hudu har lahira.

Maharan sun bude wa dan siyasar wuta ne bayan kammala sallar Juma'a, yayin da yake ganawa da jama'a a kofar gidan mahaifinsa.

Wasu mutanen hudu ciki har da tsohon shugaban Karamar Hukumar Ngala - wanda kani ne ga gwamnan jihar Ali Madu Sharif da wani karamin yaro da kuma mai wanke takalmi, duka sun hallaka a harin.

Alhaji Modu Fannami Gubio, shi ne wanda gwamnan jihar ke marawa baya domin ya gaje shi a zaben da za a gudanar a watan Afrilu.

An dade ana fama da tashin hankali a jihar ta Maiduguri wanda ake alakanta wa da kungiyar Boko Haram.

Amma wakiliyar BBC a jihar Bilkisu Babangida, ta ce ana alakanta wannan da ma kashe-kashen baya-bayan nan da siyasa.