An harbe dan takarar gwamnan Borno

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na cewa a yammacin Juma'a ne wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka harbe dan takarar gwamna a karkashin tutar jam'iyar ANPP mai mulkin jihar, Alhaji Modu Fannami Gubio har lahira.

Kimanin mutane hudu ne 'yan bindigar su ka harbe tare da shi.

Ciki har da yayan gwamnan Borno wanda ya taba rike mukamin shugaban Karamar Hukumar Ngala wato Alh Goni Modu Sheriff yayin da mutane biyu suka jikkata.

Lamarin dai ya faru ne a kofar gidan Mahaifin marigayin dake unguwar Shehuri cikin Karamar Hukumar Birnin Maiduguri da kewaye, lokacin da 'yan bindigar da ke kan babura suka bude musu wuta.