Mandela: Mutum mafi kima a duniya

Mandela Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mandela na da kima a idon duniya sosai da sosai

Matsayin Nelson Mandela na wanda ya fi kowa kima a duniya ba abin shakku ba ne. Amma duk da haka kwadayinsa na kawo sauyi ta fuskar siyasa na nan a tare da shi.

Wannan matsayi na sa ya tabbata ne ta fuskoki da dama, ciki har da kyaututtuka sama da dari da ya samu da kuma sunayensa da aka sanya a wurare daban-daban na duniya.

Shugabannin duniya da dama da kuma shahararrun 'yan wasa kamar su Michael Jackson da David Beckham da Mohammed Ali duk suna fatan a gansu tare da shi.

A karshen rayuwarsa ya maida hankali ne wajen samar da zaman lafiya a nahiyar Afrika da neman ganin an samar da kudade wajen yaki da cutar HIV/Aids da ilimi da kuma talauci.

Mai samar da zaman lafiya

Baya ga jawabin da ya yi ga Majalisun dokokin Burtaniya da kuma shan shayi da Shugaban Amurka na wancen lokaci Bill Clinton, ya ziyarci kasashe da dama domin gode wa wadanda suka taimawa jam'iyyar ANC.

Ya jagoranci shirin samar da zaman lafiya karkashin Kungiyar hada kan kasashen Afrika - a yanzu Tarayyar Afrika, a kasashen da dama ciki har da Angola da Burundi.

Ya kuma nuna adawa da mamayar da Amurka ta yiwa Iraqi a shekara ta 2003.

Tarihi ba za a manta da nasarorin da Mandela ya samar a duniya ba.

Baya ga Nelson Mandela Children's Fund da Mandela Foundation da sauran cibiyoyi na bincike kan HIV/Aids, ya kuma kafa Mandela Rhodes Foundation wacce ke bada tallafin karatu ga 'yan Afrika ta Kudu.