An saka dokar hana yawon dare a Masar, yayinda zanga zanga ta kazamta

Masu zanga zanga da yansandan a Masar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga da yansandan a Masar

Shugaba Hosni Mubarak na Masar ya kafa dokar hana yawon dare a birnin Alkahira da Alexandria da kuma Suez yayinda mummunar zanga zangar kin jinin gwamnati ta kara kamari.

Yansandan kwantar da tarzoma sun yi amfani da barkonon tsohuwa da albarusan roba domin tarwatsa masu zanga zangar da ke son ganin Shugaban ya yi murabus.

An ga motocin soji a kan hanyar birnin Alkahira. An kashe akalla mai zanga zanga guda a artabu a birnin Suez mai tashar jiragen ruwa.

Wakilin BBC a Alkahira ya ce babban kalubale ne ga ikon Shugaba Mubarak.

Ya ce dakarunsa nada karfi to amma masu zanga zangar -- wadanda lamuran da suka faru Tunisia ke kara wa kwarin guiwa -- na kara dakewa.

Rahotanni kuma sunce an cunna wuta a kan hedikwatar Jama'iyar dake mulkin kasar ta NDP a Alkahira.

Haka nan kuma a yankin Suez, masu zanga-zangar sun dira a kan ofishin yan 'yansanda, suka kwashi makamai, suka kuma cinna ma gidan wuta.

Tunzurin, wanda ba saba gani ba a Masar din, ya biyo bayan kwanki ne da aka kwashe ana zanga-zanga, wadda aka kashe akalla mutane takwas a ciki.

Babbar kungiyar adawa ta 'yan uwa Musulmi ta ce za ta goyi bayan zanga-zangar ta yau duk da dai ba ta umarci magoya bayanta su fito kan tituna ba.

A daren jiya dai wani lauyan kungiyar ya ce mahukunta sun kama jiga-jiganta gudu hudu tare da wasu mabiya.

Wasu rahotanni na cewa an yi ta samun matsalar amfani da yanar gizo da wayoyin tafi da gidanka.

Wasu mutanen dai sun bayyana cewa sam sun kasa shiga shafukan yanar gizo, yayin kuma da wasu ke bayyana wasu matsalolin na daban.

Yanar gizo wato internet dai ta taka mahimmiyar rawa wajen hado kan masu zanga zanga a duk kasashen larabawa ciki har da kasar Masar, lamarin da ya yi ta janyo zanga zanga ta kwana da kwanaki.

Matsalolin da aka samu na kasa shiga shafukan yanar gizon dai zai iya takaita wasu jerin zanga zangar da ake kokarin shiryawa nan gaba.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta bayyana cewa za ta dauki gagarumin mataki akan duk wani wanda ya tada zaune tsaye bayan an idar da Sallar Juma'a.