Tashin hankali a Plateau da Kogi

Jami'an tsaro a Najeriya
Image caption Jami'an tsaro a Najeriya

Rahotanni daga Jos, babban birnin jihar Plateau, sun ce an sami hasarar rayuka a sanadiyar tashin hankalin da aka yi a birnin a yau.

Rahotannin sun ce tashin hankalin ya fi kamari ne a unguwannin Farar Gada, da Hanyar Zariya da kuma Sabon Layin Rusau, inda aka kafsa musamman tsakanin matasa, tare da kona dimbin dukiya.

A jahar Kogi ma an ce mutum guda ya rasa ransa, bayan da aka yi wata arangama tsakanin 'yan sanda da wasu samari masu zanga-zanga a garin Kabba.

Samarin na nuna rashin amincewarsu da matakin da gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Idris ya dauka, na bari a gina jami'ar gwamnatin tarayya a Lokoja, babban birnin jihar, sabanin yadda suka yi zato.

Matasan dai na son a gina jami'ar ne a garin Kabba.