Ranar karshe a yakin neman zabe a Nijar

Tutar Nijar
Image caption Tutar Nijar

Yan takarar shugabancin kasa a Jamhuriyar Niger sun gudanar da gangaminsu na karshe a yau, gabanin zaben shugaban kasar da aka shirya yi a jibi litinin.

Yakin neman zaben ya mayar da hankali akan batutuwa kamar rage talauci da yiwa tattalin arzikin kasar garanbawul da matsalar tsaro. Shugabannin gwamnatin mulkin sojan kasar, wadanda suka yi alkawarin mayar da mulki ga hannun farar hula bayan da suka hambarar da gwamnatin Tandja Mamadou, kusan shekara guda da ta wuce, su ne suka shirya wannan zabe.

Idan har kamar yadda aka yi hasashe babu wani dan takarar da ya samu sama da kashi 50 na kuri'un a zagaye na farko, to za a je ga zagaye na biyu a zaben.

Tuni dai wasu jam'iyyun siyasa 6 suka kulla kawance domin mara wa dayansu baya idan har an je zagaye na biyu.

'Yan takara 10 ne za su kara a zaben shugaban kasar.