Shugabannin Kasashen Afirka zasu gana a Addis Ababa

Taron shugabannin kasashen Afirka AU
Image caption Shugabannin kasashen Afirka zasu gana a kasar Habasha domin tattauna rikice rikicen da kasashen yankin ke fama dasu

Kusan yanzu ne ake sa ran shugabannin kasashen Afirka zasu soma taron kwanaki biyu na kungiyar tarayyar Afurka, a Addis Ababa, babban birnin kasar Ethiopia.

Ana dai sa ran cewa shugabannin zasu tattauna batutuwa da dama da suka hada da rikicin kasar Masar, da Tunisia, da Somalia da kuman kasar Ivory Coast.

Gabanin soma taron shugaban hukumar kungiyar ta AU, Jean Ping yace, dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar ta AU dake Somalia zasu iya maida martani ga duka wani yunkurin masu tada kayar baya na kifar da gwamnatin Somalia, idan har kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya basu damar yin hakan.