'A tinkari rikicin Cote d'Ivoire gaba daya'

Ban Ki-moon Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ban Ki-moon

Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya yi kira na neman hada karfi da karfe domin maganin rikicin siyasar da ake fama da shi a Cote D'voire.

A yayin da ya ke jawabi ga taron koli na kungiyar Tarayyar Afirka, Mr Ban ya ce akwai bukatar kungiyar da Majalisar Dinkin Duniya su yi aiki tare, domin tabbatar da an dora Mr Alassane Ouattara a matsayin halataccen shugaban kasar Cote D'voire.

Mr Ban Ki-moon, ya ce duk wani matakin da za a dauka, ya kamata yayi tasiri a dukan fadin duniya.

Dubban 'yan Cote d'Ivoire ne dai suka yi gudun hijira zuwa kasashe makwabta domin gudun tashin hankali, sakamakon rikicin siyasar da ya ki ci ya ki cinyewa.