Tashin hankali a Jos da Maiduguri

Jami'an tsaro a Maiduguri
Image caption Jami'an tsaro a Maiduguri

Wasu 'yan bindiga sun kaiwa wani wurin duba masu wucewa na 'yan sanda hari a Maiduguri inda suka hallaka wani dan sanda.

Hukumomin 'yan sanda sun ce an kashe biyu daga cikin wadanda suka kai harin, bayan musayar wutar da aka yi tare da su.

Birnin na Maiduguri dai na fuskantar karuwar tashe tashen hankula daga kungiyar nan ta Boko Haram.

A halin da ake ciki kuma an samu rahotannin da ke cewa yawan mutanen da suka hallaka a rikicin da aka yi jiya asabar a Jos sun kai ashirin da daya.

Kungiyar Jama'atu Nasril Islam da ke garin na Jos ta ce, an yi jana'izar mutane 15, a yayin da wata kungiyar agaji ta Krista ta ce an gano gawar Kiristoci 6 akan tituna.