Sirikin Zine al-Abidine Ben Ali na neman mafaka a Canada

Tsohon shugabankasar Tunisia Zine Al Abidene bn Ali Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani sirikin tsohon shugabankasar Tunisia ya tsere zuwa kasar Canada inda yake neman a bashi mafaka a kasar

Gwamnatin kasar Canada tace, wani kusa a rusashshiyar gwamnatin Tunisia, wanda kuma hamshakin attajiri ne, mai suna Belhassen Trabelsi ya nemi mafaka a kasar ta Canada.

Shi dai Mista Trabelsi, sirikin tsohon shugaban kasar Tunisian, ya isa birnin Montreal dake gabacin Canadan tare da iyalansa, bayan ya tserewa rikicin da ya kifar da gwamnatin ta Tunisia.

Sai dai ministan harkokin wajen Canadan yace dole ne a bi dokar kasa kafin a bashi mafakar, abinda kuma yace zai iya daukar shekara da shekaru

Tuni dai sabuwar gwamnatin kasar Tunisian ta bada umarnin a tuso keyarsa zuwa gida.

To sai dai babu irin wannan yarjejeniya ta tusa keyar mutanen da suka tsere tsakanin gwamnatin Tunisia data Canada

Wakilin BBC yace jami'an gwamnatin Canada dai sun yi tananata cewar, basa marhabun da zuwan Mista Trabelsi kasarsu, domin kuwa yana cikin jami'an tsohuwar gwamnatin Tunisia da ake zargi da aikata cin hanci da rashawa.