Jajibirin babban zabe a jamhuriyar Nijar

Janar Salou Djibo, Shugaban mulkin sojan Nijar
Image caption Janar Salou Djibo, Shugaban mulkin sojan Nijar

A jamhuriyar Nijar gobe Litinin ne idan Allah ya yarda ake gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki.

Yan takara sun gudanar da gangaminsu na karshe a jiya Asabar.

Yakin neman zaben ya mayar da hankali akan batutuwa kamar rage talauci da yiwa tattalin arzikin kasar garanbawul da matsalar tsaro. Shugabannin gwamnatin mulkin sojan kasar, wadanda suka yi alkawarin mayar da mulki ga hannun farar hula bayan da suka hambarar da gwamnatin Tandja Mamadou, kusan shekara guda da ta wuce, su ne suka shirya wannan zabe.

Idan har kamar yadda aka yi hasashe babu wani dan takarar da ya samu sama da kashi 50 na kuri'un a zagaye na farko, to za a je ga zagaye na biyu a zaben.

Tuni dai wasu jam'iyyun siyasa 6 suka kulla kawance domin mara wa dayansu baya idan har an je zagaye na biyu.

Jama'a a Nijar na cigaba da bayyana fatansu game da irin shugabannin da suke son ganin sun jagorance su a nan gaba.

'Yan takara 10 ne za su fafata a zaben na gobe.