Zanga zangar adawa da gwamnatin Sudan

Shugaba Omar al-Bashir Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Omar al-Bashir

Masu zanga zanga a Khartoum babban birnin kasar Sudan, sun yi arangama da 'yan sanda a lokacin wani gangami na nuna rashin amincewa da gwamnati.

Ana ganin wadanda suka shirya shi, sun samu karfin guiwa ne daga zanga zangar da ake yi a kasar Masar da ke makwabtaka da Sudan din.

Masu zanga zangar, wadanda akasarinsu dalibai ne, suna korafi ne akan tsadar farashin kayan abinci.

Suna kuma kira ga Shugaban da ya dade yana mulki a kasar, Omar Al-Bashir, da yayi murabus.

'Yan sandan sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga zangar, inda kuma suka kama wasu masu yawa.

Masu zanga zangar sun shaidawa BBC cewar 'yan sandan sun yi musu duka sosai.

Shugaba Omar al-bashir ya mayar da martani ta hanyar korar Darektan jami'ar birnin Khartoum.