An kafa sabuwar gwamnati a Masar

Hosni Mubarak Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar Masar

Shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya rantsar da sabuwar majalisar ministocinsa yayinda jamaa ke cigaba da zanga-zanga a Alkahira, suna neman ya yi murabis.

Babban sauyin da aka samu a gwamnatin, shi ne yadda aka maye gurbin ministan al'ammuran cikin Gida, wanda ya yi kaurin suna, Habib el Adly.

Masu zanga-zangar dai na dora ma shi alhakin bada umarni ga 'yan sanda don yin amfani da karfi a kansu, fiye da kima.

Hakanan ma, an sauke ministan kudi, Youssef Boutros-Ghali.

Sai dai an sauya mukamai ne kawai ga ministan tsaro da na na harkokin waje. A halin da ake ciki kuma, rundinar sojin kasar ta Masar ta ce ba za ta yi amfani da karfi a kan masu zanga-zangar ba