An yi zanga zanga a Jos

Gwamnan Jihar Filato
Image caption Jonah Jang, Gwamnan Jihar Filato

Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato a Nijeriya sun cewa an yini ana ta zanga-zanga game da tashe-tashen hankula da ake fuskanta a jihar ta filato.

Masu zanga-zangar sun fito ne a kan tituna daban-daban suna bayyana bukatunsu da kuma ra'ayoiynsu cikinsu lumana yayin da jami'am tsaro suka kasance cikin shirin ko ta kwana.

An dai gudanar da zanga-zangar ce kashi biyu.

A kashi na farko wasu mata ne masu yawa suka yi jerin gwano daga Filin Polo zuwa gidan gwamnatin jihar dake unguwar Tudun Wada domin nuna rashin jin dadinsu da yadda jami'an tsaro ke aikinsu a jihar.

A kashi na biyu kuwa wasu jama'a ne suma masu yawan gaske suka hau kan tituna suna bukatar a kawar da gwamnan jihar Jonah Jang daga mulki domin a samu zaman lafiya a jihar.