Ana babban zabe a Jamhuriyar Nijar

Zabe a Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zabe a Nijar

A jamhuriyar Nijar ana cigaba da kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki.

Masu zabe kimanin miliyan 7 ne zasu zabi shugaban kasar daga cikin 'yan takara 10, da kuma 'yan majalisar dokoki 113.

Zaben ne ake fatan zai kawo karshen ikon gwamnatin rikon kwarya wadda majalisar mulkin sojan CSRD ke jagoranta tun bayan kifar da gwamnatin Malam Mamadou Tandja.

Sai dai duk da tabbacin da hukumomin kasar, musamman ma hukumar zabe mai zaman kanta suka bada, na cewa sun dauki matakan gudanar da zabe mai tsafta, wasu 'yan takarar shugabancin kasa sun soma korafin cewa ana shirya masu wata makarkashiya.

Rahotanni daga sassa dabam dabam na kasar na nuna cewa ana zaben cikin kwanciyar hankali.

Sai dai a wurare irinsu Maradi da Zinder ana fuskantar matsalar sayar da kuri'u, yayin da ake zargin wasu 'yan siyasa da yin jinga da masu zabe.

A jahar Tahoua rahotanni sun ce, wasu mutane dauke da makamai sun kwace akwatunan zabe masu yawa daga jami'an zaben, a yankin Tchintabaraden.