Yau ake zaben shugabankasa dana 'yan majalisar dokoki a Nijar

Zabe a jamhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yau 'yan jamhuriyyar Nijar zasu zabi sabon shugabankasarsu da kuma 'yan majalisar dokoki, a wani yunkuri na maida kasar bisa tafarkin damukradiyya

A yau ne jama'a zasu fito domin zabar shugaban kasa, da kuma 'yan majalisar dokoki a Niger, kuma wanan zabe ne da zai maida kasar bisa turbar dimukradiyya.

Dama dai shugabannin mulkin sojan kasar da suka kifar da gwamnatin Mamadou Tandja, kusan shekara guda da ta gabata, sun yi alkawarin maida ikon kasar hannun fara hula.

Mutane goma ne dai ke takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyu daban-daban.

Niger dai na daga cikin kasashen duniya da suka fi fama da talauci, kuma dukkanin jam'iyyun sun tabo batun yaki da talauci a yakin neman zabensu.

Wakilan BBC a jamhuriyar Nijar sun ruwaito cewar tuni wasu tawaggar masu sa ido akan yadda zaben zai gudana suke iso kasar. An kuma baza jami'an tsaro a dukkanin rumfunan zabe