'Ina nan a Tripoli -Shugaba Gaddafi

Kanar Muammar Gaddafi Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Kanar Muammar Gaddafi yana magana ta gidan talabijin

Shugaba Gaddafi na Libya ya bayyana a gidan talabijin na kasar a karo na farko tun bayan barkewar rikice-rikice kusan mako guda da ya gabata.

Da misalin karfe biyun dare ne dai gidan talabijin din ya nuna hoton Kanar Muammar Gaddafi yana zaune a cikin wata mota rike da lema.

Mutane da dama dai sun sa ran shugaban na Libya zai yi wani dogon jawabi wanda a ciki zai yi kakkausar suka a kan kasashen Yammacin Duniya, to amma hakan ba ta samu ba.

Jawabin na Kanar Gaddafi na tsawon dakika ashirin da tara ne kacal, yana cewa yana nan a Tripoli.

“Na je dandalin Green Square don yin magana da matasa in kuma kasance da su a daren nan sai ga ruwan sama.

“Wannan alama ce ta nasara; don haka na ke so na tabbatar musu cewa ina nan a Tripoli, ba a Venezuela ba.

“Kada ku amince da abin da wadannan tashoshin talabijin din ke fada”, inji Gaddafi.

Babu wata alama da ta nuna cewa hoton da gidan talabijin din ya nuna ba a Tripoli aka dauke shi ba, kamar yadda babu wata alamar da za ta iya tabbatar da cewa a can aka dauka.

Ranar Litinin ne dai aka bayar da rahoton samun baraka a gwamnatin kasar ta Libya bayan da wadansu jakadun kasar suka bayyana cewa sun yi murabus, yayinda rahotanni suka ce Shugaba Gaddafi na kan hanyarsa ta zuwa Venezuela.