'Za a yi zabe lafiya a Najeriya' -INEC

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban Hukumar Zabe, Farfesa Attahiru Jega

A Najeriya, duk da damuwar da mutane da dama ke nunawa dangane da tabarbarewar harkokin tsaro a kasar—abin da ake ganin zai iya yin kafar ungulu ga zabubbukan da ake shirin yi a watan Afrilu mai zuwa—Hukumar Zabe mai Zaman Kanta, INEC, ta ce tana da kwarin gwiwar al'amura za su tafi kamar yadda aka tsara.

A wani taron manema labarai da ya kira a daren jiya Litinin a Abuja, Shugaban Hukumar Zaben, Farfesa Attahiru Jega, ya ce suna tattaunawa da jami'an tsaron kasar domin ganin an yi zabukan lami lafiya.

“Mun san [yanayi zai inganta] saboda muna tattaunawa da jami’an tsaro a bangarori daban-daban—abin day a kai mu ga kafa kwamitin tuntubar juna na tsaro a matakan tarayya, da jihohi, da kuma kananan hukumomi.

“Ganin irin matakan da aka dauka ya zuwa yanzu, muna da kwarin gwiwa cewa za a samu gagarumin ci gaba ta fuskar tsaro kafin lokacin da jama’a za su fita domin kada kuri’unsu”.