Mutane 36 sun rasu yayin bikin takutaha

Taswirar Mali
Image caption Taswirar Mali

Jami'an kasar Mali sun ce mutane talatin da shida sun rasu sanadiyyar turmutsutsun da ya faru a wani taron Mauludi a Bamako, babban birnin kasar.

Rahotanni kuma sun ce wasu mutanen saba'in sun jikkata.

Jama'ar dai sun cika ne a filin wasa na Modibo Keita mai daukar mutane dubu ashirin da biyar domin bikin zagayowar ranar Takutaha.

Akasarin wadanda abin ya shafa dai mata ne wadanda ke jiran samun tabarrakin Imam Osman Madani Haidara.