Amurka ta gargadi gwamnatin Libya

Hillary Clinton Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta yi kira ga gwamnatin Libya ta kawo karshen “zubar da jinin al'ummar kasar”.

A wata sanarwa da ta fitar, Misis Clinton ta ce hankalin kasashen duniya ya tashi dangane da abin da ke faruwa a Libya.

A cewarta, lokaci ya yi da za a kawo karshen zubar da jinin da ake yi wanda ba za a amince da shi ba.

Shi ma dai Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon, ya bayyana bacin ransa da jin cewa ana amfani da jiragen saman yaki na kasar ta Libya don kai hari a kan masu zanga-zanga.

A halin da ake ciki kuma, jakadan Libya a Amurka, Ali Aujali, ya ce ba zai iya ci gaba da wakiltar Muammar Gaddafi da gwamnatinsa ba.

“Daga yau al'ummar kasata na ke wakilta.

“Na wakilci gwamnatin Gaddafi tsakani da Allah har tsawon shekaru arba'in, amma ganin yadda gwamnatin da nake wakilta take kashe al'ummata, ba ni da zabi illa na ce a kai kasuwa”.

Tun da farko dai jami'an diflomasiyyar Libya a Majalisar Dinkin Duniya sun juyawa gwamnatin tasu baya suna cewa tana aiwatar da kisan kare-dangi.

Karin bayani