Zanga-zangar neman sauyi a Masar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Masu yiwa gwamnatin Masar bore sun yi kira ga jama'ar kasar kimanin miliyan guda su fito domin yin zanga-zanga a birnin Alkahira, a ci gaba da neman kawo karshen gwamnatin shugaba Hosni Mubarak.

Tuni dai rundunar sojin kasar ta bada sanarwar cewar, ba za ta yi amfani da karfin soji ba akan masu zanga-zangar.

Dubun-dubatar 'yan kasar Masar ne ke ci gaba da zanga-zanga a kan titunan kasar domin nuna rashin amincewarsu da gwamnatin shugaba Hosni Mubarak.

Kuma wannan bore shi ne mafi muni cikin shekaru talatin da shugaban ya shafe a kan karagar mulki.

Musabbabin bore

To ko me ya janyo wannan bore, kuma me hakan ke nufin ga kasar ta Masar dama yankin gabas ta tsakiya da kuma sauran kasashen Afrika baki daya?

Dr. Hussaini Abdu na kungiyar Action Aid, kuma mai sharhi a kan al'amuranMas yau da kullum ya ce kasar Masar kasa ce da ta dogara da Amurka da yammacin Turai;

"Masar kan samu kusan dala biliyan biyu a kowacce shekara, shugabannin kasar basu damu da tattalin arzikin kasar ba, saboda sun dogara ne kawai da noma da kuma yawon bude ido."

"Wadannan basu isa su daukaka rayuwar al'ummar kasar Masar ba domin ita ce mafi girma daga cikin kasashen Larabawa, kuma shi yasa take samu tallafi daga Amurka da kasashen Turai.

Saboda a ganinsu Masar ce kawai za ta iya tabbatar da zaman lafiya a yankin saboda girman Sojinta."

Ya kara da cewa Mubarak ya fi kowanne Shugaban Afrika dadewa a kan mulki, a inda yake mulki na tsawon shekaru talatin.

Yawancin matasa ne ke zanga-zangar, kuma wasu tun kafin a haife su Mubarak ke kan mulki.

"Suna ganin ana zabe kuma a sauya shugabanni a wasu kasashen amma ban da Masar".

Mahimmacin Masar

A lokutan 1960, Masar na taka mahimmiyar rawa a cikin kasashen Larabawa, musamman a fagen diflomasiyya da kuma tsaro.

Amma a yau, bayan shekaru 50, masu taka rawa a yankin Gabas ta Tsakiya su ne kasashen da ba na Larabawa wato Isra'ila da Turkiyya da kuma Iran.

Duk da haka Masar na da tasiri ba wai kawai saboda tarihi ba. Girmanta da kuma karfin sojinta ya sa tana da karfin fada aji a yankin.

Kuma a yanzu tana daya daga cikin kawayen Amurka na kud-da-kud, ita ke biye ma Isra'ila a wajen samun taimakon soji daga Amurka.

Sai dai tana fama da matsalolin da sauran kasashen yankin ke fama da ita: talauci; karuwar yawan matasa, rashin aikin yi da karancin tsarin dimokradiyya.

An kifar da gwamnati a Tunisia, kuma al'amura sun ci gaba a yankin. Idan aka kifar da gwamnatin Hosni Mubarak, to lamarin zai zama abin duba wa.

Karin bayani