Ana ci gaba da zanga-zanga a Masar

Ana ci gaba da zanga-zanga a Masar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga na taruwa a dandalin Tahrir da ke birnin Alkahira

Masu zanga-zanga a Masar su ce suna fatan mutane miliyan guda za su fito kan tituna a ci gaba da yunkurinsu na kawar da gwamnatin Hosni Mubarak.

Wadanda suka shirya zanga-zangar sun ce suna fatan hada mutane miliyan guda wanda shi ne adadi mafi girma tun bayana fara. A garin Iskandariyya ma ana shirya makamancin wannan boren.

Rundunar sojin kasar mai karfin fada aji, ta ce ba za ta yi amfani da karfi kan masu zanga-zangar ba.

Wakiliyar BBC Lyse Doucet da ke dandalin Tahrir, ta ce dandazon jama'ar da ya hadu a dandalin ya haura na kwanakin baya.

Jim kadan bayan sojan kasar ta Masar sun ce, ba zasu yarda a yi amfani da su wajen murkushe jama'a ba.

Sabon mataimakin shugaban kasar ta Masar, Omar Suleiman ya bayyana a gidan talabijin inda yace, an bashi damar ya soma tattaunawa da dukkan bangarorin siyasar kasar a kan yadda za'a kawo sauyi a siyasance.

Ya kuma ce, za'a sake zaben 'yan majalisar dokoki a wasu lardunan da aka samu shaidun tafka magudi a zaben da ya gabata.

Karin bayani