Sarki Abdullah na Jordan ya kori gwamnatinsa

Masu zanga-zanga a Jordan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga a Jordan

Sarki Abdullah na Jordan ya kori gwamnatinsa sannan ya baiwa sabon Pirayim Ministansa Marouf Bakhit umurnin gudanar da sauye sauyen siyasa.

Hakan ya biyo bayan wata babbar zanga -zanga a ko'ina cikin kasar a cikin watan Janairu game da fatara da rashin aikin yi da kuma bukatun cewar a rinka zabar Pirayim Minista kai tsaye.

Sai dai Kungiyar adawa ta Islama, ta ce ba ta neman hambarar da Sarki Abdullah.