An sace mahaifiyar wani dan takarar Senata a Kebbi

Wasu jami'an 'yan sandan Nijeriya
Image caption Wasu jami'an 'yan sandan Nijeriya

'Yan sanda a jahar kebbin Najeriya sun ce jami'ansu na can na bin sawun wasu 'yan bindiga da suka sace mahaifiyar dan takarar majalisar dattawa na jam'iyyar Adawa ta CPC daga gidanta dake garin Yawuri a daren jiya.

Wata majiyar iyalan Hajiya Fatima Ahmed sun ce mutanen sun yi awon gaba da ita ne da bakin bindiga zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba.

Matar dai ita ce mahaifiyar Alhaji Sadik Ahmed Yelwa dan majalisar dattawa ta kudancin jahar.

Matsalar sace-sacen mutane dai tana neman zama ruwan dare a Nijeriya, kuma al'ammarin na tayar wa da al'umma hankali, musamman ma ganin cewa zabe na karatowa.