Masu saka ido sun yabi zaben Nijer

Hakkin mallakar hoto AFP

A jamhuriyar Niger kawancen masu sa ido a zaben da aka gudanar, na kungiyar Tattalin Arzikin Africa ta yamma ECOWAS/ CEDEAO sun ya yabi yadda aka gudanar da zabe a kasar cikin tsanaki.

Masu sa idon na cewa, an gudanarda wannan zabe a cikin kwanciyar hankali, in banda 'yan kurakurai da ba a rasa ba.