Zanga-Zanga ta kara kamari a Masar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

An gudanar da zanga zanga mafi girma tun fara tashin tashina a Alkahira inda dubban mutane suka kwarara zuwa dandalin Tahrir suna neman Shugaba Hosni Mubarak da ya yi murabus.

Yayinda dare ya fadi, taron mutane, ya fara ragewa, to amma wakilin BBC a can ya ce a fili take da yawa na shirin kashe dare a waje, duk kuwa da dokar hana yawon dare wadda a badini take aiki.

Taron jama'ar sun yi ta karkada tutoci suna rera taken kasa sannan suna kururuwar nuna kin jini ga Shugaba Mubarak.