Mahaukaciyar guguwa da ruwa a Australia

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wata mahaukaciyar guguwa mai hade da ruwa da ake kira Cyclone Yasi ta afkarwa yankin arewacin gabar tekun Queensland.

Guguwar cyclone Yasi ta afkarwa gabar tekun Queensland ne da tsakar daren su na jiya.

Wannan ta kasance daya daga cikin guguwa masu muni da suka taba faruwa a tarihin Australia.

Guguwar ta yi ta'adi sosai musamman a garin Tully, sai dai duk da haka babu rahoton cewa mutane sun jikkata sosai.

Karfin iskar na tafiya ne nisan kimanin kilomita dari biyu da chasa'in a sa'a guda.

Da yake an yi ta gargadin samun guguwa mai muni a tarihin kasar, tuni mutane suka watse daga garuruwan da ke nan kusa.

Dubban mutanen dake zaune a can sun yi kaura zuwa wadansu sansanonin 'yan gudun hijira.