Fada ya barke a dandalin Tahrir na kasar Masar

Fada ya barke tsakanin masu zanga-zanga a Masar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dandalin Tahrir nan ne wajen da masu zanga-zangar ke fafatawa

An bada rahotannin barkewar fada a dandalin Tahrir na kasar Masar, tsakanin magoya bayan shugaba Hosni Mubarak da kuma masu adawa da shi.

Rahotanni sun ce jama'a da dama sun samu rauni tsakanin bangarorin biyu, bayan da suka dinga jifan junansu.

Dubban magoya bayan shugaba Mubarak ne sun isa dandalin na Tahrir, suna kawar da shingayen da masu adawa da shi suka sanya.

Hakan ya biyo bayan sanarwa da sojojin kasar suka bayar ne, ta cewa mutane su koma gida domin al'amura su koma yadda suke. Shugaba Mubarak ya yi alkawarin ba zai tsaya takara a zaben watan Satumba ba.

Sojojin dai ba su shiga tsakanin masu zanga-zangar ba.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya ce lallaine a fara sauyi cikin kwanciyar hankali "nan take", yayin da Fira Minstan Turkiyya Erdogan ya ce ya kamata Mr Mubarak "ya dauki wata hanyar daban".

"An saurari sakonnin ku, bukatarku ta fito fili..... Za ku iya mayar da al'amura yadda suke," Kamar yadda mai magana da yawun sojin ya fada a gidan talabijin din kasar.

A bangare guda kuma, hanyoyin sadarwa na intanet da wayar salula sun fara koma wa daidai bayan da gwamnati ta katse su na wasu kwanaki.

Karin bayani