Jam'iyyu bawai ba za su tsaya takara a Najeriya ba

Hukumar zaben ta INEC ta ce ta amince da sunayen 'yan takarkarun da wasu jam'iyyu goma sha biyu suka gabatar mata, wadanda a baya ta yi watsi da su bayan da suka saba wa'adin da aka dibar musu na mika sunayen.

Hukumar ta ce ta dauki matakin ne domin baiwa kowa damar taka rawa a cikin harkokin zabe.

Daga cikin jam'iyyun akwai jam'iyyar (ADC) da (PAC), da (ACD) da (AA) da (JP) da(NAP). Sauran sun hada da (FPN) da (DPP) da (KP) da (NPC) da (NMDP) da (MDJ).

Hukumar ta kara da cewa tun da Jam'iyyu bawai sun gaza mika mata sunayen 'yan takarar ta su, hakan na nufin ba za a dama da su a zaben da za a gudanar a watan Afrilu ba.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa suna da damar damawa a zabukan da zasu biyo bayan wadanda za'a yi a watan Afrilun bana.