Za'a soma kwaso 'yan Najeriyar dake kasar Masar a yau

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Gwamnatin Najeriya zata soma aikin kwaso 'yan kasar daga Kasar Masar daga yau

A Najeriya, gwamnatin tarayya ta ce a yau ne zata fara aikin kwaso 'yan kasar da ke kasar Masar, sakamakon zanga-zangar da ake yi don neman tilastawa shugaban kasar Hosni Mubarak ya sauka daga kan mulki.

Dubban 'yan Najeriya ne dai suke da zama a kasar ta Masar, kuma gwamnati ta ce fiye da mutane dari biyu daga cikinsu sun nuna aniyyarsu ta dawowa gida don gujewa hatsaniyar da ake yi a kasar.

'Yan Najeriya mazauna kasar Masar ne dai sukai kira ga gwamnatin tarayyar Nijeriya da ma gwamnatocin jihohi dasu dauki matakin tallafa musu saboda halin da aka shiga a kasar, sakamakon zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da ake yi.

'Yan najeriyar sun koka ga jinkirin da ake samu wajen kwaso su, suna masu cewar tuni gwamnatocin wasu kasashen suka fara aikin kwaso 'yan kasarsu da suka makale a kasar

Wannan zanga zanga dai ta tilastwa mutane da dama hadi da baki 'yan yawan bude ido tserewa daga kasar ba tare da shiri ba.