Ana cigaba da samun sakamakon zabe a Nijar

Zabe a Jamhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumar zaben Nijar na cigaba da tattara sakamakon zaben shugabankasa dana 'yan majalisar dokoki

Hukumar zaben Nijar CENI ta bayyana cewar ya zuwa yanzu ta samu kashi sittin cikin dari na sakamakon kuri'un da aka kada na 'yan majalisar dokokin kasar

Hukumar CENI tace shi kuwa zaben shugabankasa, ta sami kashi arba'in cikin dari na kuri'un da aka kada kawo i yanzu

Shugaban hukumar zaben mai shari'ah Ghousman Abdurahman ya shaidawa BBC cewar yawancin sakamakon zaben yazo hannunsu, kuma yace ana tsammanin zasu kammala samun dukkanin sakamakon zaben kasar a yau

Shugaban hukumar ya kuma tabbatar da cewar an samu wasu kura kurai a wasu jahohin kasar irinsu Maradi da Tileberi, abinda yace ya kaiga cafke wasu mutane.

Hukumar zaben tace an cafke mutane13 a Maradi kadai, yayin da a jihar Tawa kuwa, wasu mutane dauke da makamai suka hana yin zaben a wasu rumfuna

Hukumar zaben tace za'a gurfanar da wadannan mutane a gaban kotu domin su fuskanci shari'ah