Amurka tace Masar na bukatar sauyi nan take

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Barack Obama na Amurka yace kasar Masar na bukatar sauyi nan take cikin lumuna

Shugaba Obama na Amurka, yace, dole ne a soma daukar matakan kawo sauyi a kasar Masar, cikin lumana, kuma a soma shi nan take.

Shugaba Obama ya fadi hakan ne jim kadan bayan shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak yayi jawabi ga al'ummar kasar inda yace, zai sauka daga kan karagar mulki, amma idan wa'adinsa ya kare

Mr Obama ya kuma ce 'yan kasar Masar nada 'yancin fadin albarkacin bakinsu, tare kuma da 'yancin walwala

Shugaba Obama ya kuma ce yana yabawa rundunar sojan kasar Masar saboda irin kwarewa da kuma kishin kasa da suka nuna wajen barin 'yan kasar su cigaba da zanga-zanga cikin lumana.