Gwamnatin Kamaru za ta kyautata farashin abinci

Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya ya bayyana daukar matakin shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki.

Shugaban ya kafa wata hukuma da zata rinka shigo da kayayyakin abincin daga kasashen ketare domin a sayarwa wa jama'a a farashi mai rahusa.

A yanzu haka dai kayan masarufi, kamar sukari da sabulu, da shinkafa da kuma danyen kifi, farashin su ya hau sama sosai.

Mutanen kasar, wadanda ke ta korafin tashin farashin kayan abincin, sun bayyana farin cikinsu da duk awani shiri da zai rage masu farashin kayan abincin.