Shugaba Mubarak ya ce zai sauka idan wa'adi ya cika

Hakkin mallakar hoto AP

Dubban 'yan kasar Masar sun shafe tsawon dare akan titunan Alkahira, inda masu zanga zangar adawa da gwamnatin kasar ke shirin gudanar da wani gagarumin gangami kan shugaban kasar Hosni Mubarak yayi murabus.

Shugaban dai na fuskanta matsin lamba sosai, na yayi murabus daga wurin masu zanga zangar adawa da shi, fiye da mako guda kenan.

Sai dai kuma Mista Mubarak din ya bayyana cewa zai sauka daga mulki idan wa'adin mulkin sa ya kare.

Ya kara da cewa idan ya sauka yanzu, duk da cewa yana son yin murabus din, akwai yiwuwar hargitsi ya afku, kuma kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood wato Jam'iyyar Islamar da aka sanyawa takunkumi a kasar Masar, za ta karbi iko,.

A bangare guda kuma Majalisar dinkin duniya ta fara kwashe ma'aikatanta da ke aiki a kasar.

Kawo yanzu kimanin ma'aikatan ta dari uku ne suka bar kasar, kuma ana saka ran wasu za su bi sawu.

Wani mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniyar ya bayyana cewa yanayin da ke akwai a kasar ta Masar babu tabbaci akansa, sannan kuma matsaloli kamar na rashin hanyoyin sadarwa musamman na internet ya sanya aiki yana musu wuya a can.

Tashin hankalin dake faruwa a kan titunan kasar dai ya sanya Magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar ya yi wani jawabi.

Ya dai bayyana cewa harin da ake kaiwa masu zanga zangar lumanar da kuma cin zarafin 'yan jaridu da magoya bayan shugaba Husni Mubarak ke yi abune da ba za'a amince dashi ba.