Mata musulmi sun yi zanga zanga a Jos

A jihar Filato ta Nijeriya daruruwan mata musulmi sun shirya wata zanga-zanga ta lumana a birnin Jos inda ake samun rikice rikice na addini da kuma kabilanci.

Matan sun ce su na so ne su nuna bakin cikinsu game da al'amurran da ke faruwa a jihar, da kuma halin ko- in- kula da suke zargi hukumomi da nunawa.

Masu zanga zangar sun nemi a sauke gwamnan jihar Pilto, Jonah Jang.

Wani kakakin gwamnan ya yi watsi da kiran da suka yi yana cewa a sauke shi.