Shehun Borno ya nemi da ayi azumin kwana uku

A jihar Borno dake Arewacin Najeriya, an yi wani taron ganawa da manyan malamai, da Bulamomi, da Lawanai, da masu unguwannin tare da Mai Martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al'amin El-Kanemi.

An kira taron ne domin fuskantar matsalolin da ake fama da su na yawan hare-hare da kashe-kashen dake faruwa a birnin Maiduguri.

Daga bisani ne Mai Martaba Shehun Bornon ya kira taron manema labarai inda ya fitar da sanarwa ga jama'ar Jihar da su yi kokarin yin azumin kwanaki uku daga gobe asabar domin cigaba da addu'oin Allah ya kawo wanzuwar zaman lafiya a tsakanin al'ummar jihar.

Al'ummar gari kuma sun yi kira ga jami'an tsaro da su kara kaimi wajen basu kariyar da ta kamata.