Wasu 'yan Jam'iyyar CPC sun kai Jam'iyyar kara

A Najeriya wasu `ya`yan Jam`iyyar adawa ta CPC sun shigar da karar uwar Jam`iyyar a wata kotun tarayya a Abuja.

'Ya'yan Jam'iyyar suna zargin uwar Jam`iyyar ne da sauya sunayensu da na wasu, a lokacin da take mika wa hukumar zabe sunayen `yan takarar ta na babban zabe mai zuwa.

Masu karar dai wadanda suka hada da wadanda suka shiga zaben fid-da-gwani na mukamin Gwamna a jihohin kano da Katsina da wasu mukamai, sun ce sun je kotu ne domin bin hakkinsu.

Amma jam`iyyar CPC a nata bangaren, ta ce tana iya soke zaben ko wanne dan takara idan ta fahimci ya saba da ka`ida wajen neman mukamin nasa.

Wannan na faruwa ne kuma bayan da cikar wa'adin da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ware domin mika mata sunayen 'yan takara.

A bangare guda kuma Jam'iyyar ADC, na zargin hukumar INEC ne da sauya ka'idojin mika sunayen 'yan takara sa'o'i kadan kafin cikar wa'adin, kuma ta sha alwashin gurfanar da hukumar gaban kotu matukar ta dage kan kin karbar sunayen 'yan takararta.

Sai dai hukumar zaben ta musanta zargin, ta na mai cewa su hadu a kotu.