Zanga zangar kin jinin gwamnati a Yemen

A Yemen, dubun dubatar jama'a sun yi zanga zangar nuna adawa da gwamnati a Sanaa, babban birnin kasar, inda suke neman shugaba Ali Abdullah Saleh ya yi murabus, bayan ya kwashe fiye da shekaru talatin yana mulki.

Masu zanga zangar sun hallara a kusa da jami'ar Sanaa, inda suke ta wake-waken a kawo karshen cin hanci da rashawa, da kuma mulkin kama karya a kasar ta Yemen.

Daya daga cikin masu zanga zangar ya ce suna son sauyin siyasa, da kuma alkawarin kwatanta gaskiya.

Suna kuma son zaman lafiya da 'yanci.

A jiya Laraba, shugaba Ali Abdullah Saleh ya ce, ba zai sake yin takara ba, bayan cikar wa'adin mulkinsa a shekara ta dubu biyu da goma sha ukku, ko kuma ya mika mulki ga dansa.

Magoya bayansa sun shirya kishiyar zanga zanga, inda suke yin kira a gare shi da ya ci gaba da mulki.