Ana ci gaba da zanga zangar adawa a Masar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A Kasar Masar dubban masu zanga zanga sun shafe tsawon dare a dandalin Tahrir dake tsakiyar birnin Alkahira, bayan wani gagarumin gangamin da suka yi inda suke neman shugaban kasar Husni Mubarak ya yi murabus.

Masu zanga zangar sun yi ta daga tutar kasar tare da rera wakokin kishin kasa, a cikin daren jiya.

To amma wani dan adawa ya shaidawa BBC cewa watakila masu zanga zangar su ragu a dandalin, inda za su rika gudanar da zanga zangar a ranakun Talata da Jumua, amma a sauran kwanaki ba za su rika fitowa sosai ba.

Ya kara da cewa, lokaci yayi da za a bari mutane su koma ga harkokinsu na yau da kullum.

Yayinda zanga zangar ke ci gaba, akwai alamun cewa ana samun nasara wajen tursasawa Mista Mubarak da ya sauka daga karagar mulki.